Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsoratar da masu zuba jari na ƙasashen waje, duk da ikirarin da take yi na samun daidaiton tattalin arzikin Najeriya.

Obi ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi tsokaci kan rahoton yanayin zuba jari na Najeriya na shekarar 2026 da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar.

Ya ce rahoton ya nuna cewa cin hanci da rashawa, rashin tsaro, rashin tabbas wajen aiwatar da dokoki, raunin tsarin shari’a, matsalolin wutar lantarki da jinkirin fitar da kaya daga tashoshin jiragen ruwa na daga cikin matsalolin da ke rage sha’awar masu zuba jari a Najeriya.

A cewar Obi, rahoton ya kuma yi gargaɗi kan yiwuwar tsare ’yan kasuwa ba bisa ƙa’ida ba, hana tafiye-tafiye da amfani da dokokin shige da fice wajen matsa wa kamfanonin ƙasashen waje lamba.

Ya ce jinkirin fitar da kaya daga tashoshin Apapa da Tin Can na iya wuce kwanaki 20, duk da cewa tashar Lekki ta taimaka wajen rage matsin lamba.

Obi ya ce ya kamata rahoton ya sa gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan gaggawa domin binciken matsalolin da aka gano tare da magance su, musamman ganin yadda Najeriya ke buƙatar jawo jarin kai-tsaye daga ƙasashen waje.

Ya bayyana cewa daga cikin dala biliyan 10.37 na jarin waje da aka shigo da su Najeriya a zangon farko na shekarar 2026, dala miliyan 135.08 ne kawai suka kasance jarin kai-tsaye, yayin da kusan dala biliyan 9.86 suka shiga kasuwannin hannayen jari.

Obi ya yi zargin cewa gwamnatin APC ce ke da alhakin matsalolin da ke hana Najeriya jawo masu zuba jarin da ya dace da damar tattalin arzikinta.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *