Gwamnatin Mauritius ta sanya dokar hana fita a yankuna 10 na ƙasar daga yammacin Talata zuwa safiyar Laraba, bayan barkewar zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali sakamakon harbin wata mata da ɗan sanda ya yi.

Rahotanni sun ce ɗan sanda ya harbi wata matar a wuya ba tare da gargaɗi ba, lamarin da ya jikkata ta sosai. An kama ɗan sandan kuma an gurfanar da shi a gaban kotu, yayin da likitocin Indiya suka yi nasarar cire harsashin da ke jikinta, an ce Matar na ci gaba da karɓar magani a asibiti.

Zanga-zangar ta fara ne tun kafin harbin, inda masu zanga-zangar suka yi amfani da tayoyin mota masu cin wuta wajen toshe hanyoyi, sakamakon ƙarancin ruwa da tsadar rayuwa.

Bayan harbin, an samu rahotannin satar kayayyaki a wasu manyan shaguna da kai hare-hare kan ofisoshin ’yan sanda, inda wasu jami’ai suka jikkata.

Firaministan ƙasar, Navin Ramgoolam, ya yi gargaɗin cewa gwamnati za ta gano waɗanda suka haddasa tashin hankalin tare da ɗaukar matakan da suka dace a kansu.

Ofisoshin jakadancin Birtaniya da Faransa sun kuma gargaɗi ’yan ƙasashensu da ke Mauritius da su guji wuraren zanga-zanga da tarukan jama’a, tare da yin taka-tsantsan.

Sai dai wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ba a samu sabon tashin hankali ba tun bayan saka dokar hana fita a yammacin Talata.

Mauritius, wadda ta samu ’yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1968, ta daɗe tana samun ci gaban tattalin arziki, musamman ta fuskar yawon buɗe ido, masana’antar tufafi da harkokin kuɗi.

Sai dai annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikinta illa bayan da ta taɓa shiga rukunin ƙasashen masu babban matsayi na samun kuɗin shiga a shekarar 2020.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *