Hichilema ya yi wannan kiran ne a yayin buɗe taron kwamitin Ministocin Ƙasashen Yankin na Ƙungiyar Ƙasashen yankin tafkin Afirka (ICGLR), karo na 20 wanda aka gudanar a Otal ɗin InterContinental da ke Lusaka, babban birnin Zambia.
Shugaban ya bayyana cewa rashin damar shiga harkokin tattalin arziki, da rashin aikin yi da ƙarancin damarmakin ci gaba na daga cikin abubuwan da ke haddasa rashin kwanciyar hankali.
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta rage yawan ruwan da ke wurin da jirginta ya faɗi a Jihar Ondo
- ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara takwas sun koma APC bayan sun gana da Shugaban Kasa Bola Tinubu
Ya ce ƙasashen yankin za su iya magance waɗannan matsaloli ta hanyar zuba jari tare, ƙarfafa kasuwanci tsakanin iyakokinsu da amfani da albarkatun yankin yadda ya kamata.
Ya kuma buƙaci ƙasashen mambobin ICGLR su riƙa fifita saye da sayar da kayayyaki a tsakaninsu, musamman kayan amfanin gona, kafin neman irin waɗannan kayayyaki daga ƙasashen da ke wajen yankin.
Hichilema ya ce manufofin Zambia na ƙara samar da masara, waken soya, alkama da sukari na iya taimakawa wajen inganta wadatar abinci da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki a yankin.
Game da harkar haƙar ma’adanai, shugaban ya jaddada buƙatar gudanar da ita bisa doka, cikin aminci da kuma hanyar da ta haɗa kowa, tare da kare ma’aikata da muhalli.
Ya ce ya kamata al’ummomin da ke zaune a wuraren da ake haƙar ma’adanai su amfana daga albarkatun da ake samu a yankunansu.
Ya kuma buƙaci ƙungiyar ICGLR ta wuce gudanar da tarurruka kawai, ta hanyar samar da takamaiman matakai masu ma’aunin tantance nasara a fannonin bunƙasa tattalin arziki, wadatar abinci da sarrafa albarkatu.
A cewarsa, ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya a kowace ƙasa na taimakawa wajen bunƙasa yankin baki ɗaya.
Hichilema ya ƙara da cewa ajandar Grow Zambia ta ƙasarsa tana da alaƙa da ci gaban ƙasashe 12 da ke cikin ƙungiyar, yana mai cewa haɗin gwiwa da amfani da albarkatu yadda ya kamata za su taimaka wajen magance tushen rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.