Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta buƙaci limamai da ƙungiyoyin addinin Musulunci su ƙara wayar da kan jama’a kan cutar Ebola, biyo bayan tabbatar da bullarta a Najeriya.

A cikin sanarwar da ta fitar ranar 21 ga Oktoba, 2026, majalisar ta ce gano cutar da wuri, samun kulawar lafiya cikin gaggawa da bin matakan kariya na da muhimmanci wajen rage yaɗuwarta, duk da cewa babu takamaiman maganin warkar da nau’in Bundibugyo da aka amince da shi.

Ta bayyana cewa Ebola na yaɗuwa ta hanyar taɓa jini ko ruwan jikin mai cutar, kayayyakin da suka gurɓata ko gawar wanda ya mutu sanadiyyar cutar.

Alamominta sun haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, kasala, amai da gudawa.

Majalisar ta buƙaci duk wanda yake zargin ya kamu da cutar ya nemi taimakon hukumomin lafiya cikin gaggawa, tare da guje wa hulɗa da sauran mutane.

Ta kuma bayyana cewa jama’a na iya kiran layin gaggawa na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta lamba 6232.

Haka kuma, ta bukaci limamai su yi wa jama’a wa’azi kan Ebola a hudubar Juma’a, tare da jaddada tsaftar hannu da guje wa taɓa gawar wanda ake zargi ya mutu sanadiyyar cutar.

Ta ce ma’aikatan lafiya da aka amince da su ne ya kamata su gudanar da jana’izar cikin aminci.

Sanarwar, wadda Sakataren Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya sanya wa hannu, ta kuma bukaci Musulmi su guji yaɗa jita-jita da nuna wariya ga waɗanda cutar ta shafa.

Majalisar ta jaddada cewa kare rayuka da neman magani sun dace da koyarwar Musulunci.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *