
Ta yaya Ebola ta bazu?
Ba a tabbatar da cikakken tushen kamuwa da cutar a kowane mutum ba, amma masana sun bayyana cewa cutar Ebola na iya shiga jikin mutum ta hanyar kusanci da wasu dabbobin da ke ɗauke da ƙwayar cutar, sannan ta yaɗu daga mutum zuwa mutum ta hanyar taɓa jini ko sauran ruwan jikin wanda ya kamu da ita.
Haka kuma, mutum na iya kamuwa da ita ta hanyar amfani da kayayyakin da suka gurɓata da ruwan jikin mai cutar.
Saboda haka, rashin gano masu cutar da wuri, tafiye-tafiye da kuma kusanci da masu fama da ita ba tare da kariya ba na iya taimakawa wajen yaɗuwarta.

Tarihin Ebola a Yammacin Afirka
An fara samun bullar cutar Ebola a Yammacin Afirka tsakanin shekarun 2014 zuwa 2016, musamman a ƙasashen Guinea, Laberiya da Saliyo.
Bullar ta kasance mafi girma a tarihin cutar, inda aka samu fiye da mutane 28,600 da suka kamu da ita, sai dai yaɗuwar ta wancan lokaci ba ta nufin ita ce tushen bullar shekarar 2026; sabuwar bullar cutar ta samo asali ne daga DRC, kuma tana da alaƙa da wani nau’in ƙwayar cutar daban, wato Bundibugyo.

Me ya faru a Uganda da Kenya?
A Uganda, an tabbatar da bullar cutar a shekarar 2026 bayan samun mutanen da suka shigo daga DRC, an samu mutane 20 da suka kamu da cutar, ciki har da 15 daga DRC, kuma mutane biyu sun mutu.
Amma a ranar 27 ga Agusta, hukumar lafiya ta WHO ta sanar da kawo ƙarshen cutar bayan shafe kwanaki 42 ba tare da samun sabon wanda ya kamu da ita ba, sai dai daga baya, Kenya ta tabbatar da shigowar cutar ta hannun wani mutum da ya fito daga DRC ta Uganda zuwa Nairobi.
Mutumin ya mutu a ranar da aka tabbatar yana ɗauke da cutar, kuma daga baya adadin waɗanda suka kamu a Kenya ya kai tara, bisa bayanan da hukumar lafiyar kasar wallafa a ranar 20 ga Oktoba.

Yadda Ebola ta shiga Najeriya
A ranar 20 ga Oktoba, 2026, hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa wata mata da ta shigo Najeriya daga Uganda ta kamu da Ebola mai nau’in Bundibugyo.
Alamomin cutar sun fara bayyana a jikinta ranar 7 ga Oktoba, kwanaki huɗu bayan isowarta Najeriya, sannan ta nemi magani a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja a ranar 11 ga Oktoba.
Gwajin dakin binciken ranar 20 ga Oktoba ne ya tabbatar da ta kamu da cutar, nan take aka killace ta domin ba ta kulawar lafiya, yayin da hukumomi suka gano mutane 44 da suka yi mu’amala da ita, waɗanda ake sa ido kan lafiyarsu.
Har yanzu ana gudanar da bincike domin gano inda ta kamu da cutar da kuma cikakken tarihin tafiye-tafiyenta.

Me ya sa cutar ta iya ketare iyakoki?
Babban dalilin da ya sa cutar ke bazuwa zuwa ƙasashe daban-daban shi ne tafiye-tafiyen mutane kafin a gano cewa suna ɗauke da ita.
Bullar cutar a baya-bayan nan, an ga yadda tafiya daga DRC ta Uganda zuwa Kenya ta shigar cutar Kenya, yayin da wata mata da ta dawo Najeriya daga Uganda ta kamu da ita.
Jinkirin gano alamomi da tabbatar da cutar na iya ba ta damar kaiwa wuraren da ba a shirya fuskantar ta ba.
Sai dai duk da haka, wannan ba yana nufin duk wanda ya yi tafiya daga ƙasashen da cutar ta shafa zai kamu da ita ba; sai an yi bincike da gwaji domin tabbatar da hakan.

Ta yaya za a kare kai da sauran jama’a?
Ebola ba ta yaɗuwa kamar mura ta hanyar zama kusa da mutum kawai ba tare da wani irin hulɗa ba.
Ana kamuwa da ita musamman ta hanyar taɓa jini ko sauran ruwan jikin mai cutar, ko kayayyakin da suka gurɓata da waɗannan ruwan.
Alamomin farko sun haɗa da zazzabi, gajiya, ciwon kai, ciwon tsoka da maƙogwaro, sannan wasu marasa lafiya na iya samun amai ko gudawa.
Duk wanda ya fara samun alamomin da ke tayar da hankali, musamman bayan yiwuwar hulɗa da mai cutar ko tafiya daga yankin da cutar ta shafa, ya nemi taimakon lafiya cikin gaggawa kuma ya sanar da ma’aikatan lafiya game da tarihin hulɗarsa da tafiye-tafiyensa.
Bai kamata a yi hulɗa kai tsaye da jinin ko ruwan jikin wanda ake zargi da cutar ba.