Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce haɗa tsarin B’Odogwu da dandamalin National Single Window zai zama mataki na gaba wajen inganta sarrafa takardun cinikayya da kuma gano mutane da kayayyakin da ke da haɗarin tsaro a iyakokin ƙasar.
Kwanturola-Janar na hukumar, Adeniyi, ya bayyana shirin ne yayin gabatar da lacca mai taken “Muhimmancin Kwastam: Kuɗaɗen Shiga, Tsaro da Ƙasa a Duniyar da Ba Ta da Iyakoki” a Jami’ar Ibadan ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026.
Ya ce amfani da fasahar zamani ya taimaka wajen mayar da ayyukan hukumar na dijital, rage amfani da takardu da kuma ƙarfafa tsaron takardun hukuma, ba tare da hana gudanar da kasuwanci tsakanin ƙasashen yankin ba.
- WHO ta bukaci a inganta kula da lafiyar matan da suka daina al’ada
- Ƙungiyar mata masu goyon bayan Tinubu ta kai ziyara ga Ministan Yaɗa Labarai
Adeniyi ya bayyana cewa haɗa tsarin biyu zai ba masu harkokin kasuwanci damar gabatar da dukkan takardun da suka shafi cinikayya ta dandamali guda.
Ya ƙara da cewa fasaha za ta taimaka wajen nazarin yadda abubuwa ke faruwa da hasashen barazanar tsaro, tare da inganta ƙwarewa da nagartar jami’an hukumar.
A nasa jawabin, shugaban Jami’ar Ibadan, Farfesa Kayode Adebowale, ya ce Kwastam na taka muhimmiyar rawa wajen kare ikon ƙasa, dokokinta da tsaronta.
Ya bayyana hana shigo da jabun kayayyaki da makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma tarwatsa hanyoyin fasa ƙwauri, a matsayin matakan kare ƙasa.
A wani ɓangare na ziyarar, Adeniyi ya gana da Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, wanda ya nuna aniyarsa ta haɗa kai da hukumar wajen yaƙi da safarar kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba, laifukan da suka shafi ƙetare iyakoki da kuma tabbatar da zaman lafiya a al’ummomi.