Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce menopause, wato lokacin da mace ke daina al’ada har abada, wani mataki ne na halitta da mata ke shiga yayin tsufa, inda ta bukaci a inganta wayar da kai da kuma kula da lafiyar matan da ke fuskantar sauye-sauyen.
WHO ta bayyana cewa mafi yawan mata na shiga wannan mataki ne tsakanin shekaru 45 zuwa 55, sakamakon raguwar aikin ƙwai da saukar sinadarin oestrogen a jiki. Ana tabbatar da menopause idan mace ta shafe watanni 12 a jere ba tare da ganin al’ada ba, kuma babu wani dalili na lafiya da ya haddasa hakan.
Hukumar ta ce sauye-sauyen kan fara ne a hankali, inda al’ada za ta fara canza tsari kafin ta tsaya gaba ɗaya. Wannan lokacin, wanda ake kira perimenopause, na iya ɗaukar shekaru da dama, kuma yana iya shafar lafiyar jiki, tunani, yanayin zuciya da rayuwar zamantakewar mace.
- Yadda Ebola ta bazu zuwa Yammacin Afirka har ta shigo Najeriya
- NSCIA ta bukaci limamai su wayar da kan jama’a kan Ebola
Daga cikin alamomin da mata kan fuskanta akwai jin zafi kwatsam a fuska da wuya da ƙirji, zufa da daddare, rashin barci, sauyin yanayi, damuwa, bushewar farji da jin zafi yayin saduwa. Haka kuma, raguwar sinadarin oestrogen na iya ƙara haɗarin raunin ƙashi da wasu matsalolin lafiya.
WHO ta jaddada cewa akwai hanyoyin magani na hormonal da waɗanda ba na hormonal ba da za su iya rage waɗannan matsaloli. Ta bukaci matan da ke fuskantar alamomin da ke shafar rayuwarsu su tuntubi ma’aikatan lafiya domin samun shawarwari da kulawar da ta dace da yanayin lafiyarsu.
Hukumar ta kuma yi kira da a ƙara wayar da kan jama’a game da menopause, a horar da ma’aikatan lafiya kan yadda za su taimaka wa mata, tare da tabbatar da cewa ana samun bayanai da ayyukan lafiya masu inganci.
Ta ce kula da mata kafin, lokacin da kuma bayan menopause na da muhimmanci wajen inganta lafiyarsu da ingancin rayuwarsu yayin tsufa.