Majalisar Bincike da Bunƙasa Ilimi ta Najeriya (NERDC) ta yi gargaɗi kan yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba a shafukan sada zumunta game da sabon tsarin karatun firamare, ƙaramar sakandare da babbar sakandare.

Majalisar ta bayyana cewa an tsara sabon tsarin karatun ne bisa bincike da ƙwarewar da ake buƙata, domin inganta sakamakon karatu, rage cunkoson darussa da koyar da ɗalibai dabarun aiki da za su taimaka musu a ƙarni na 21.

Ta ce tsarin ya ƙunshi fannoni kamar fasahar dijital, koyon ƙananan na’urorin mutum-mutumi, basirar AI, sana’o’i, ilimin zama ɗan ƙasa da tarihin Najeriya.

Haka kuma, yana ƙarfafa ɗabi’u nagari, haƙuri da juna a addinai, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.

NERDC ta jaddada cewa darussan da aka amince da su su ne waɗanda ta sanar a hukumance. Ta ce an fara aiwatar da sabon tsarin ne a farkon kowane zangon karatu na shekaru uku, wato a aji ɗaya da na huɗu na firamare, JSS 1 da SSS 1.

Saboda haka, majalisar ta buƙaci iyaye, malamai, shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki su yi watsi da jerin darussan da ba a tabbatar da su ba, da jadawalin koyarwa da sauran bayanan da ake yaɗawa a intanet ba tare da sahihiyar hujja ba.

Majalisar ta buƙaci jama’a su duba shafinta na hukuma, www\.nerdc.gov.ng, domin samun ingantattun bayanai game da sabon tsarin karatun da darussan da aka amince da su.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *