Kamfanin Dangote Cement da ke Gboko, jihar Benue, ya bayar da tallafin karatu na miliyoyin nairori ga ɗaliban makarantun sakandare da manyan makarantu ga al’ummomin shida da ke maƙwabtaka da kamfanin.
Kamfanin ya kuma raba kayan fara sana’a, kayan aiki da takardun shaidar kammala horo ga matasan da suka kammala shirin ƙarfafa matasa, domin su yi amfani da ƙwarewar da suka samu wajen kafa sana’o’insu da dogaro da kai.
Ministan Bunƙasa Ma’adinai, Dakta Henry Dele Alake, ya yaba wa kamfanin kan shirye-shiryen da yake gabatarwa don ci gaban al’umma, tare da kira ga sauran kamfanoni masu zaman kansu su yi koyi da irin wannan tallafi.
- Babban Bankin Najeriya ya tattauna da ’yan kasuwa kan sauƙaƙa biyan kuɗi tsakanin Najeriya da China
- ’Yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Bauchi
Ya kuma buƙaci kamfanin ya ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da aka amince da su tare da al’ummomin da ke maƙwabtaka da shi.
Shugaban sashen hulɗa da al’umma na kamfanin, Wakeel Olayiwola, wanda Dakta Johnson Kor ya wakilta, ya ce shirye-shiryen tallafin karatu da ƙarfafa matasa na cikin yarjejeniyar ci gaban al’umma da kamfanin ya ɗauki nauyin aiwatarwa, domin koyar da sana’o’i, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.
Mukaddashin Daraktan masana’antar Gboko, Injiniya Arbind Singh, wanda Injiniya Tabershima Soom ya wakilta, ya ce tallafin karatu na shekara-shekara na nuna ƙudirin kamfanin na sauke nauyin da ke kansa na taimaka wa al’umma.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 150 da manoma 50, inda aka ba mata kuɗaɗen bunƙasa sana’o’i, manoma kuma aka ba su kayan aikin gona.
Al’ummomin da suka amfana sun haɗa da Tse-Kucha, Quarry, Amua, Mbazembe, Mbatur da Pass Brothers.
Wakilan gwamnati da sarakunan gargajiya sun yaba wa kamfanin, yayin da ɗaya daga cikin matasan da suka amfana, Ignatius Aondohemba, ya ce zai yi amfani da kayan aiki da ƙwarewar da ya samu wajen kafa sana’ar da za ta ba shi damar ɗaukar wasu aiki.