Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, Abuja, ta yanke wa wani tsohon jami’in Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Oluwole, hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari kan bayar da takardar bogi da ta taimaka wajen biyan kuɗin magungunan da ba a kawo ba.
Mai shari’a Yusuf Halilu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuffuka masu alaƙa da shi (ICPC) ta gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume biyu na bayar da bayanan ƙarya yayin gudanar da aikinsa na hukuma.
Oluwole, wanda ya taɓa aiki a matsayin babban jami’in tantance hajojin kaya a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, ya bayar da takardar shaidar kammala tantance kaya ga kamfanin Mubaraq Pharmacy Limited a watan Mayun 2015, yana tabbatar da cewa an kawo wasu magunguna alhali ba su iso Najeriya ba.
- ’Yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Bauchi
- Gwamnatin tarayya ta amince da ɗaga darajar jami’an tsaro sama da 27,000
- Kamfanin Dangote ya ware miliyoyin nairori don tallafawa karatun ɗalibai a Benue
ICPC ta bayyana cewa takardar mai lamba CA 0329 ta taimaka wajen biyan kamfanin kuɗi har Naira miliyan 29,996,120 kan zargin samar da allurar Ribavirin guda 5,113 da ƙwayoyin maganin Globavirin guda 5,681.
Kotun ta tabbatar da cewa ba a kawo magungunan ba a lokacin da Oluwole ya tabbatar da karɓarsu.
A tuhume-tuhume biyun, an zargi Oluwole da bayar da bayanan ƙarya da kuma miƙa bayanan ƙarya ga tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Linus Awute.
Laifukan sun saɓa wa sashe na 16 da sashe na 25(1)(a) na dokar yaƙi da cin hanci da rashawa ta shekarar 2000.
Kotun ta same shi da laifi a tuhume-tuhume na farko, ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000 a tuhume-tuhume na biyu.
Mai shari’a Halilu ya kuma umarci a kai shi gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja domin ya fara zaman gidan yari.