Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwato kayan da ake zargin tabar wiwi, da wasu ƙwayoyin magunguna ne.
An kama mutanen ne a samame daban-daban da jami’an rundunar suka gudanar a ranar 21 ga Oktoba, 2026.
A samamen farko, jami’an Sashen Yaƙi da Laifuka Masu Tsanani (VCRU) sun kama wani mutum mai shekaru 29 a Mararaban Liman, Katagum. Binciken da aka gudanar a wurin ya kai ga ƙwato ƙunshin tabar da ake zargin wiwi ne guda 124, ƙwayoyin Tramadol mai nauyin miligram 100 guda 12 da ƙwayoyin Exzol guda 50.
- Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya gargaɗi sababbin jami’ai kan rashin gaskiya lokacin aiki
- Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su rungumi AI ba tare da karya ƙa’idojin aikin jarida ba
Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa kayan da aka ƙwato na wani mutum da ake kira G-Man ne, wanda ya tsere kuma jami’an tsaro ke ƙoƙarin gano inda yake.
A wani samamen kuma, jami’an sun kama wani mutum mai shekaru 31 a yankin Bayan Gari da ke cikin birnin Bauchi, bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi.
A hannunsa ne aka samu buhunan ƙwayoyi guda 14 da wasu adadin busassun ganyayyaki da ake zargin tabar wiwi ne.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ce ana ƙara ƙaimi wajen gano wanda ya tsere da kuma sauran masu hannu a safarar kayan.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake tsare a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai.