Gwamnatin Tarayya ta amince da ɗaga darajar jami’an tsaro sama da 27,000 a hukumomin tsaro huɗu na rundunonin sa-kai, tare da inganta manufofin kula da lafiyarsu.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan bayan taron Hukumar Kula da Ayyukan Tsaron Farar Hula, Gidajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da Shige da Fice (CDCFIB).
Hukumar ta kuma amince da wani cikakken tsarin kula da lafiyar jami’an, wanda aka tsara domin inganta lafiyarsu, ƙarfinsu da walwalarsu. Ministan ya ce matakan za su taimaka wajen ƙarfafa gwiwar jami’ai da kuma inganta ayyukansu.
- Gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin yaɗa labarai su faɗaɗa wayar da kan jama’a kan Ebola
- Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya gargaɗi sababbin jami’ai kan rashin gaskiya lokacin aiki
Dangane da ɗaukar sababbin ma’aikata, Tunji-Ojo ya ce gwamnatin tarayya ta sake jaddada aniyarta ta ɗaukar matasa ’yan Najeriya 120,000 a hukumomin tsaron cikin wa’adin mulkinta na farko.
Ya bayyana cewa aikin ɗaukar rukunin farko na mutane 30,000 na ci gaba, inda za a buɗe shafin neman aikin daga ranar 28 ga Oktoba zuwa 13 ga Nuwamba, 2026.
Ministan ya ce jimillar jami’an da aka ɗaga darajarsu a hukumomin huɗun tun bayan hawan mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta zarce 100,000.
A cewarsa, an ɗaga darajar jami’ai sama da 32,000 a shekarar 2023, sama da 20,000 a 2024, fiye da 24,000 a 2025, sannan sama da 27,000 a sabon matakin da aka amince da shi a 2026.
Tunji-Ojo ya ce waɗannan matakai na ma’aikatar suna da nufin magance tsaiko wajen samun ƙarin girma a aiki, tare da samar da ƙwararrun jami’ai masu ladabi da ƙoshin lafiya waɗanda za su iya sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu.