Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya umarci hukumomin yaɗa labarai na tarayya su ƙara wayar da kan jama’a kan cutar Ebola, bayan tabbatar da bullar cutar a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), Gidan Talabijin na Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), Muryar Najeriya (VON) da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).
Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafinsu ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da bullar cutar a wata mata da ta zo daga Uganda zuwa Abuja.
- Atiku ya nemi Tinubu ya yi bayanin kan Naira biliyan 10 na yaƙi da Ebola
- Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su rungumi AI ba tare da karya ƙa’idojin aikin jarida ba
A cewar sanarwar, an killace ta kuma tana karɓar magani, yayin da hukumomin lafiya ke bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da ita.
Ministan ya ce gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin shawo kan lamarin da kare lafiyar ’yan Najeriya.
Ya buƙaci hukumomin su isar da sahihan bayanai cikin harsuna daban-daban, musamman kan yadda cutar ke yaɗuwa, hanyoyin kariya da wuraren kai rahoton waɗanda ake zargin sun kamu da ita.
Ministan ya kuma umarci hukumomin su yi aiki tare da Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a da NCDC domin tabbatar da sahihancin bayanan da za su yaɗa.
An kuma buƙaci NOA ta haɗa kai da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin al’umma da kafafen yaɗa labarai wajen wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar.
Gwamnatin ta buƙaci ’yan Najeriya su kwantar da hankulansu, su dogara da bayanan hukumomin hukuma, tare da guje wa yaɗa jita-jita a kafafen sada zumunta.