Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya na adana tarihin rundunar wanzar da zaman lafiya ta ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOMOG) da kuma sadaukarwar da jami’anta suka yi.
Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar tsoffin sojojin ECOMOG ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Ohifeme Ejimai (mai ritaya), a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja.
Janar Musa ya ce Najeriya ta kashe makudan kuɗaɗe tare da tura jami’an tsaro da dama domin gudanar da ayyukan rundunar.
- Najeriya da Rwanda sun ƙarfafa haɗin gwiwar soji don magance matsalolin tsaro a Afirka
- NERDC ta yi gargaɗi kan yaɗa bayanan ƙarya game da sabon tsarin karatu
Ya jaddada cewa ba za a manta da sojojin da suka rasa rayukansu, musamman a ayyukan wanzar da zaman lafiya a Laberiya da Saliyo ba.
Ya kuma tabbatar wa tawagar cewa za a kammala ƙoƙarin tattara ragowar bayanai, sunayen waɗanda suka mutu da sauran muhimman kayayyakin tarihi da suka shafi rundunar, domin adana su yadda ya kamata ga al’ummomin da za su zo nan gaba.
Tun da farko, Manjo Janar Ejimai ya bayyana halin da tsoffin sojojin Najeriya da suka tsira daga ayyukan ECOMOG suke ciki, yana mai cewa a shirye suke su ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban ƙasa da tsaro.
Ya buƙaci Ma’aikatar Tsaro ta magance gibin da ke cikin bayanan tarihi tare da duba yiwuwar ware rana ta musamman domin tunawa da daruruwan sojojin Najeriya da suka mutu wajen tabbatar da zaman lafiya a Afirka ta Yamma.
An kafa ECOMOG a shekarar 1990 ƙarƙashin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) domin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya da tabbatar da shi a yankin.
Rundunar, wadda Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen jagorantarta, ta taimaka wajen dawo da tsarin mulki, kare fararen hula da daidaita yankunan da rikice-rikice suka shafa.