Malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Ayuba Lukuwa, ya zargi gwamnatin Jihar Sakkwato da bayar da umarnin sakin wani mutum da ya kira Mai Barewa, wanda ya ce ya yi barazanar kashe shi.
Sheikh Lukuwa ya bayyana hakan ne a wani saƙo na musamman da ya aikawa mabiya Ahlussunnah, inda ya ce gwamnatin jihar ce za ta ɗauki alhakin duk wani rikici da ka iya ɓarkewa sakamakon matakan da ake ɗauka kan lamarin.
Malamin ya yi zargin cewa an saki Mai Barewa duk da cewa ya ce mutumin ya sake tabbatar da barazanar da ake zarginsa da yi masa, lokacin da aka gabatar da shi a gaban jami’an tsaro da sauran waɗanda suka halarci zaman.
- NERDC ta yi gargaɗi kan yaɗa bayanan ƙarya game da sabon tsarin karatu
- Gwamnatin Sakkwato ta kashe Naira biliyan 6.79 tallafin karatu cikin shekaru uku
Ya kuma yi zargin cewa an taɓa sakin wasu mutane 22 da ya ce sun shiga ƙone-ƙone tare da yin barazanar kisa, sai dai saƙon bai bayyana lokacin da aka saki mutanen ko cikakkun bayanan shari’o’insu ba.
Sheikh Lukuwa ya ce ba zai amince da a jira har sai an cutar da shi kafin a ɗauki mataki ba, yana mai cewa ya kamata a magance barazanar da ake zargin an yi masa.
Ya kuma yi zargin cewa siyasa na iya shigowa cikin lamarin, amma bai gabatar da hujjar da za ta tabbatar da wannan zargi ba.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu martanin gwamnatin Jihar Sakkwato kan zarge-zargen da malamin ya yi, kuma ba a samu tabbaci mai zaman kansa kan yanayin sakin mutumin da kuma zargin barazanar kisan ba.