Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kammala horas da jami’anta 160 a kwasa-kwasai shida na ƙwarewa a Cibiyar Gudanarwa ta Sojin Sama ta Najeriya (NAFIAM), da ke Otuokpoti a jihar Bayelsa, a ranar 23 ga Oktoba, 2026.
Cikin waɗanda suka kammala horaswar akwai manyan jami’ai 12 da sauran sojoji 148, maza da mata.
Wannan shi ne karo na biyu da cibiyar ta gudanar da bikin yaye ɗalibai tun bayan dauke ta daga Kaduna, inda aka horas da su a fannonin gudanar da harkokin ma’aikata, jagoranci da gudanarwa, motsa jiki, kiɗan soja da hulɗa da jama’a.
- Kamfanin Dangote ya ware miliyoyin Naira don tallafa wa karatun ɗalibai a Binuwai
- ’Yan sanda sun kama mutane uku bis
Da yake wakiltar Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, Kwamandan rundunar Mobility Command, Air Vice Marshal Michael Onyeabashi, ya bayyana kammala horaswar a matsayin wani muhimmin mataki wajen bunƙasa cibiyar.
Onyeabashi ya buƙaci waɗanda suka kammala horaswar su yi amfani da ilimin da suka samu cikin ladabi, gaskiya da ƙwarewa.
Tun da farko, kwamandan NAFIAM, Air Commodore Isaiah Taiwo, ya jaddada aniyar cibiyar na samar da ingantaccen horo wanda zai dace da sababbin buƙatun ayyukan soji.
Babban Hafsan Sojin Sama, ya yaba wa Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Sojojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayansa wajen ƙarfafa ƙwarewa da inganta ayyukan rundunar.