Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce gwamnatinsa ta kammala aikin hanyar Orlu–Mgbe–Akokwa–Uga, tare da bayyana cewa aikin na daga cikin shirye-shiryen bunƙasa ababen more rayuwa da sauƙaƙa zirga-zirga a jihar.
Uzodimma ya bayyana cewa hanyar ta fuskanci zaizayar ƙasa mai tsanani a yankin Umuchima, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa tare da katse zirga-zirga tsakanin al’ummomin yankin.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan gina gadoji da kuma shawo kan zaizayar ƙasa a yankin domin magance matsalar da ta addabi hanyar.
- ’Yan sanda sun kama mutane uku bisa zargin satar kayan aikin gona a Yobe
- Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da tashar wutar lantarki mai ƙarfin 120MVA a Kankia
A cewarsa, kammala ayyukan ya taimaka wajen rage barazanar zaizayar ƙasa, inganta tsaro ga masu amfani da hanyar da kuma dawo da zirga-zirga cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa gyaran hanyar ya taimaka wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci da kuma samar da sabbin damammaki na bunƙasar tattalin arziki a yankin da jihar Imo baki ɗaya.
Uzodimma ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan hanyoyi a matakin tarayya, jiha da ƙananan hukumomi, yana mai cewa waɗannan ayyuka na daga cikin manufofin gwamnatinsa na inganta rayuwar al’ummar jihar.