Ministan Wutar Lantarki, Joseph Olasunkanmi Tegbe, da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, sun ƙaddamar da sabuwar tashar wutar lantarki mai ƙarfin 120MVA da ke Ƙaramar Hukumar Kankia, domin ƙarfafa tsarin rarraba wutar lantarki a jihar.
Ministan ya ce aikin na daga cikin matakan gwamnatin tarayya na ƙarfafa babbar hanyar sadarwar wutar lantarki ta ƙasa da inganta ƙarfin isar da wuta zuwa ga al’umma.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da muhimman ababen more rayuwa a ɓangaren wutar lantarki.
- Inuwa Yahaya ya nemi tallafin Tinubu don bunƙasa Gombe da Arewacin Najeriya
- Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya zargi gwamnatin Sakkwato da sakin wanda ya yi barazanar kashe shi
Gwamna Radda ya bayyana kammala tashar a matsayin babban jari a fannin wutar lantarki a Katsina, yana mai cewa tashar ta ƙunshi manyan transfoma biyu, kowannensu mai ƙarfin 60MVA, waɗanda suka haɗa ƙarfin 120MVA.
Ya ce tashar za ta ƙarfafa tsarin isar da wuta a jihar tare da bai wa gidaje, kasuwanci da masana’antu damar samun ƙarin wutar lantarki.
A cewarsa, ingantacciyar wuta na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki, masana’antu da inganta ayyukan jama’a.
Gwamnan ya ƙara da cewa tashar za ta taimaka wa shirye-shiryen jihar na faɗaɗa amfani da makamashi, tare da tallafa wa noma, sarrafa amfanin gona, kasuwanci, ilimi da kiwon lafiya.
Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da aikin, tare da yaba wa Ma’aikatar Wutar Lantarki da Kamfanin Isar da Wutar Lantarki na Najeriya kan kammala shi, sannan ya buƙaci al’ummomin yankin su kare tashar daga lalatawa.