Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ƙaddamar da sabon hedikwatar Asusun Tallafa wa Tsaro na Jihar Legas (LSSTF) da ke Ikeja, domin inganta ayyukan tsaro da haɗin gwiwar hukumomin tsaro a jihar.
Sanwo-Olu ya ce tun shekarar 2007 asusun ke gudanar da ayyukansa a wani ginin haya, amma sabon ofishin hedikwatar da aka kammala cikin watanni 10 bayan fara ginin zai samar da ingantaccen wuri na tsara ayyuka da sa ido kan tsaro.
- Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya zargi gwamnatin Sakkwato da sakin wanda ya yi barazanar kashe shi
- Inuwa Yahaya ya nemi tallafin Tinubu don bunƙasa Gombe da Arewacin Najeriya
Gwamnan ya bayyana cewa ginin ya samu ne sakamakon tallafin Sir Adebukunola Adebutu Kessington, wanda ya ɗauki nauyin gina shi gaba ɗaya tare da bayar da motocin sintiri guda biyar ga asusun.
Ya gode wa hamshaƙin ɗan kasuwar bisa ci gaba da tallafa wa jihar, yana mai cewa tsaro shi ne ginshiƙin ayyukan ci gaba a Legas, kuma dole ne mazauna jihar su samu kwanciyar hankali yayin da harkokin kasuwanci ke bunƙasa.
Sanwo-Olu ya buƙaci hukumomin tsaro da za su yi amfani da ginin su inganta ayyukansu, su mutunta haƙƙin ’yan ƙasa tare da tabbatar da tsaron kowa a jihar.