Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da buɗe rajistar masu zaɓe ta wucin gadi ta shekarar 2027 a intanet, domin bai wa ’yan Najeriya damar duba bayanan rajistarsu tare da ƙara sauƙaƙa shiga tsarin tantance sahihancin bayanan masu zaɓe.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe na hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar ranar 26 ga Oktoba, 2026, INEC ta ce za a iya samun rajistar a shafinta na intanet,

Hukumar ta bayyana cewa rajistar da aka ɗora a intanet ita ce wadda aka riga aka baje kolinta a cibiyoyin rajista, kuma wannan mataki na bayar da damar samun bayanan ne domin amsa buƙatun ’yan Najeriya da masu ruwa da tsaki da suka nemi a samar da rajistar a intanet.

INEC ta ce tana ci gaba da karɓa da tantance korafe-korafe da ƙorafe-ƙorafen neman gyara da suka taso daga aikin baje kolin rajistar, bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.

An tsara kammala tantancewa da wallafa rajistar masu zaɓe ta ƙarshe a ranar 15 ga Disamba, 2026.

Rajistar ta wucin gadi na bai wa masu zaɓe damar tabbatar da cewa sunayensu da sauran bayanansu sun yi daidai, tare da gano kurakurai ko matsalolin da ya kamata a gyara kafin kammala rajistar.

Hakan na da muhimmanci wajen ƙarfafa sahihan bayanan masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

INEC ta jaddada cewa ƙara samar da rajistar a intanet na daga cikin ƙoƙarinta na inganta gaskiya, riƙon amana da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.

Ta ce masu zaɓe za su iya duba rajistar ta shafin hukumar: https://display.inecnigeria.org.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *