Marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

Shekara 20 ke nan da rasuwar Mai Alfarma Sarkin Musulmi na 19, Alhaji Muhammadu Maccido, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama a ranar 29 ga Oktoba, 2006.

Rasuwarsa ta kasance babban rashi ga al’ummar Musulmi da Najeriya baki ɗaya, amma shekaruN da suka shuɗe ba su goge tarihin gudummawar da ya bayar ga addini, al’umma da ƙasa ba.

Marigayi Sarkin Musulmi Maccido ya kasance shugaba mai son zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna. A lokacin rayuwarsa, ya yi amfani da matsayinsa wajen ƙarfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da kuma shiga tsakani wajen sasanta rikice-rikice.

Ya fahimci cewa bambancin addini ko ra’ayi bai kamata ya zama sanadin ƙiyayya ko rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma ba.

Ɗaya daga cikin abubuwan da za a ci gaba da tunawa da shi shi ne yadda ya ba da muhimmanci ga ilimi da ci gaban al’umma.

Ya nuna goyon baya ga ƙoƙarin inganta rayuwar jama’a, musamman ta fuskar ilimi, lafiya da noma. Haka kuma, ya yi amfani da matsayinsa wajen wayar da kan al’umma kan muhimman batutuwan da suka shafi rayuwarsu, ciki har da yaƙi da cutar shan inna da kare lafiyar yara.

Marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

A matsayinsa na Sarkin Musulmi, ya kasance uba ga al’umma, mai sauraron jama’a da ƙoƙarin fahimtar matsalolinsu.

Gudummawarsa ta nuna cewa shugabanci ba wai riƙe muƙami ko samun girma ba ne, illa ɗaukar nauyin jama’a, yi musu hidima da amfani da damar da Allah Ya bayar wajen inganta rayuwarsu.

Yayin da ake cika shekara 20 da rasuwarsa, abin da ya kamata al’umma su koya daga tarihin rayuwarsa shi ne muhimmancin shugabanci na gari, haƙuri, tawali’u, adalci da sadaukarwa wajen yi wa jama’a hidima.

A wannan lokaci da ƙasa ke buƙatar zaman lafiya da haɗin kai, tunawa da irin waɗannan halaye na da muhimmanci wajen gina al’umma mai fahimtar juna.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido, wanda aka haifa a ranar 20 ga Afrilu, 1926, a Dange da ke Jihar Sokoto, ya rasu a ranar 29 ga Oktoba, 2006, sakamakon hatsarin jirgin saman ADC Airlines mai lamba 053 a kusa da Abuja, yana da shekara 80 a duniya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *