Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ta buƙaci hukumomin tsaro su kama waɗanda ta zarga da kai wa ɗan takararta na gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Munir Dan Iya, hari, tare da sakin jami’an DSS guda biyu da ta ce an sace.
Jam’iyyar ta ce harin ya faru ne a daren da ya gabata a kan hanyar Airport Road da ke Sakkwato, lokacin da Dan Iya ke dawowa cikin birnin bayan ya raka tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, zuwa filin jirgin sama.
Ta zargi jami’an rundunar tsaron Sakkwato Marshals da kai harin, inda ta ce sun lalata motoci da dama a cikin tawagar ɗan takararta, ciki har da motarsa ta musamman.
- NNPC ta bukaci manya da ƙananan ’yan kasuwar mai su haɗa kai domin rage kuɗin gudanar da kasuwanci
- Shugaba Tinubu ya ce kamfanin Airtel ya ƙara tashoshin sadarwa 1,050 a Najeriya
A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC-PCC ta kuma yi zargin cewa jami’an Sakkwato Marshals sun mamaye wasu tsofaffin ƙofofin shiga birnin, suna tsare motoci da ke ɗauke da tambarin jam’iyyar tare da cin zarafin masu amfani da su.
Ta ce an kuma sace jami’an DSS biyu da ke tare da ɗan takarar.
Sanarwar ta ce Munir Dan Iya ya kai rahoton lamarin ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sakkwato.
ADC-PCC ta bayyana harin a matsayin wani nau’in tsoratar da ’yan adawa, tare da zargin cewa ana amfani da rundunar tsaron da gwamnati ke ɗaukar nauyinta wajen musguna wa masu hamayya da ita.
Jam’iyyar ta buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kwamishinan ’Yan Sandan Sakkwato da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike, su tabbatar da sakin jami’an DSS ɗin da ake zargin an sace, tare da hukunta waɗanda ke da hannu.
Ta kuma ba hukumomin wa’adin sa’o’i 24 su ɗauki matakin gaggawa, tana mai cewa za ta ɗauki wasu matakai na doka idan ba a bi buƙatunta ba.