Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da shirin Open Network na kamfanin Airtel Nigeria, tare da yaba wa kamfanin kan zuba jarin faɗaɗa hanyoyin sadarwa a ƙasar, ciki har da ƙarin tashoshin sadarwa 1,050, waɗanda 657 daga cikinsu ke amfani da fasahar 5G.
Tinubu ya ce irin wannan zuba jari na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ke ƙoƙarin jawo wa Najeriya domin ƙarfafa tattalin arziki, bunƙasa kasuwanci da samar da damarmaki ga al’umma.
- NDLEA ta ce babu kuɗin da za a biya wajen gwajin ƙwayoyi ga sabbin ma’aikatan hukumomin tsaro
- NNPC ta bukaci manya da ƙananan ’yan kasuwar mai su haɗa kai domin rage kuɗin gudanar da kasuwanci
A cikin saƙon da ya wallafa, shugaban ya bayyana cewa ingantacciyar sadarwa za ta ƙara wa ’yan kasuwa damar gudanar da harkokinsu, sauƙaƙa samun ilimi tare da bai wa ’yan Najeriya damar cin gajiyar tattalin arzikin zamani na intanet.
Ya ce gwamnati na ƙarfafa sa ido kan harkokin sadarwa, kare haƙƙin masu amfani da kuma faɗaɗa damar shiga intanet, ciki har da samar da bayanan intanet kyauta na yau da kullum ga ɗaliban da suka cancanta domin samun kayan karatu.
Tinubu ya kuma bukaci kamfanonin sadarwa su inganta ayyukansu ta hanyar faɗaɗa inda suke samun sadarwa, rage katsewar layi da inganta ingancin hidima, musamman a yankunan da har yanzu ba su da isasshen tsarin sadarwa.