Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta gudanar da taron wayar da kan ma’aikatanta kan tsaron yanar gizo na shekarar 2026, domin ƙarfafa kariyar bayanan sirri da kayayyakin sadarwa na zamani da take amfani da su.

An gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, a hedikwatar hukumar da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin sashen fasahar sadarwa da tsaron yanar gizo na hukumar.

Kwanturola Janar ta hukumar, Kemi Nanna Nandap, wadda mataimakin kwanturola janar mai kula da harkokin kuɗi da asusu, SB Daura, ya wakilta, ta jaddada muhimmancin tsaron yanar gizo wajen kare bayanan sirri, inganta tsaron ƙasa da kuma hana kutse cikin tsarin sadarwar hukumar.

Ta buƙaci jami’an hukumar su kasance masu lura da duk wani abu da ka iya zama barazana, su bi ƙa’idojin tsaro tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi da suke zargi.

Hukumar ta kuma jaddada buƙatar ci gaba da horas da ma’aikata da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin tunkarar sabbin barazanar yanar gizo.

Taron ya samu gabatar da jawabai daga ƙwararru daga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC), Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPC) da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).

Sun tattauna kan haɗin gwiwar hukumomi, yaƙi da laifukan yanar gizo, kare bayanan sirri da rage haɗarin da rashin kula da tsaro ke haifarwa a wuraren aiki.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *