Sanata Simon Bako Lalong, mai wakiltar Filato ta Kudu, ya taya tsohon gwamnan Jihar Filato, Ambasada Fidelis N. Tapgun, murnar cika shekara 85 da haihuwa.

Lalong ya bayyana Tapgun a matsayin jagora kuma gogaggen ɗan siyasa da ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’ummar Gamailand, ƙaramar hukumar Shendam, Jihar Filato da Najeriya baki ɗaya.

Ya ce rayuwar Tapgun ta ƙunshi hidimar jama’a, inda ya taɓa riƙe muƙaman gwamnan Filato, minista da jakadan Najeriya, tare da nuna jajircewa wajen gina ƙasa da inganta rayuwar al’umma.

Sanatan ya ƙara da cewa tsohon gwamnan zai ci gaba da zama abin koyi ga shugabanni ta hanyar hikimarsa, jarumta da ƙoƙarinsa wajen tabbatar da haɗin kai, adalci da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Haka kuma, Lalong ya yaba da tawali’u da kishin addinin Kirista na Tapgun, yana mai cewa ƙwarewa da gogewarsa za su ci gaba da zama jagora ga matasa da masu sha’awar ci gaban Jihar Filato da Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *