Jam’iyyar ADC reshen Jihar Sakkwato ta ce za ta ƙaddamar da kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa a jihar ranar 4 ga Nuwamba, 2026, duk da zargin fuskantar barazana da yunƙurin hana ta gudanar da harkokin siyasa.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta zargi gwamnatin Jihar Sakkwato da nuna rashin amincewa da shirin da ta yi na ƙaddamar da kamfen ɗin, wanda tun farko aka tsara gudanarwa ranar 31 ga Oktoba.
Ta ce ta sanar da gwamnatin jihar, amma ta samu amsar rashin amincewa da taron.
ADC ta kuma zargi wasu mutane da kai wa magoya bayanta mata hari yayin wani tattaki na lumana ranar 28 ga Oktoba, tare da lalata ofishin kamfen ɗinta da kayan yaƙin neman zaɓe.
- EFCC ta fayyace sharuɗɗan da masu neman aiki a hukumar za su cika
- MMPN ta yaba wa Sarkin Musulmi kan shekaru 20 na hidimarsa ga al’umma
Ta ce wasu otel-otel sun soke ajiyar da ta yi domin taron, bisa zargin matsin lamba daga gwamnati, duk da cewa ta ce tana ƙoƙarin tabbatar da wasu daga cikin rahotannin.
Game da harin da aka ce an kai wa ɗan takararta na gwamna, Manir Muhammad Dan’iya, a filin jirgin saman Sultan Sadiq Abubakar ranar 30 ga Oktoba, jam’iyyar ta zargi jami’an Sokoto Marshals da Sokoto Community Guards da hannu a kai.
Ta ce an farfasa motocin ɗan takarar, an harba bindigogi, sannan aka tsare jami’an DSS biyu da ke cikin tawagar tsaronsa.
Saboda haka, ADC ta bukaci rundunar ’yan sanda da DSS su gudanar da bincike mai zaman kansa kan dukkan abubuwan da ta ambata, su gano waɗanda suka aikata laifukan da waɗanda suka ba da umarni, tare da tabbatar da tsaron ’yan takararta da magoya bayanta.
Ta kuma nemi a tabbatar da cewa jami’an tsaron jihar ba sa amfani da muƙamansu wajen takura wa masu ra’ayin siyasa daban.
Jam’iyyar ta yi kira ga magoya bayanta da su kasance cikin natsuwa, zaman lafiya da bin doka, tana mai cewa ba za ta bari barazana ko tashin hankali su hana ta amfani da haƙƙinta na siyasa ba.
Ta kuma buƙaci ƙungiyoyin fararen hula, kafafen yaɗa labarai da ƙasashen duniya su sanya ido kan lamarin.