Ƙungiyar Ɗaliban Aikin Jarida Musulmi ta Najeriya (MMPN) ta taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulkin Musulunci, tare da yaba wa gudummawar da ya bayar wajen hidimar al’umma da ƙarfafa zaman lafiya a Najeriya.
A cikin saƙon taya murnar da ta fitar ranar 1 ga Nuwamba, 2026, ƙungiyar ta ce tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2006, Sarkin Musulmi ya shafe shekaru yana yi wa Musulunci, al’ummar Musulmi da ƙasa hidima cikin hikima da mutunci.
- Shugaba Tinubu ya yaba wa EFCC bayan FBI ta jinjina wa Najeriya
- EFCC ta fayyace sharuɗɗan da masu neman aiki a hukumar za su cika
MMPN, wadda Sarkin Musulmi yake yi wa jagoranci a matsayin babban majiɓincinta, ta bayyana jin daɗinta kan goyon bayan da yake bai wa ’yan jarida Musulmi, da kuma yadda yake ƙarfafa amfani da kafafen yaɗa labarai wajen samar da fahimtar juna da zaman tare cikin lumana.
Ƙungiyar ta ce a tsawon shekaru, Sarkin Musulmi ya yi amfani da matsayinsa wajen kira ga tattaunawa, haƙuri da mutunta juna tsakanin ’yan Najeriya masu addinai da al’adu daban-daban.
Ta kuma yaba da yadda yake ƙarfafa ’yan jarida wajen gudanar da aikinsu cikin gaskiya da ƙwarewa.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Abdur-Rahman Balogun, ya ce MMPN na haɗa kai da al’ummar Musulmi, Majalisar Masarautar Sakkwato da sauran ’yan Najeriya wajen taya Sarkin Musulmi murnar wannan matsayi, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, hikima da ƙarfin ci gaba da yi wa addini da ƙasa hidima.