Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, bayan Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta jinjina wa Najeriya kan rawar da ta taka wajen yaƙi da laifukan tilasta wa mutane yin lalata ta hanyar barazana a intanet.

A cikin sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ranar 31 ga Oktoba, 2026, an bayyana cewa yabon ya zo ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke ƙara amincewa da matakan da Najeriya ke ɗauka wajen yaƙi da cin hanci da laifukan kuɗi.

Sanarwar ta ce an cire Najeriya daga jerin ƙasashen da Hukumar FATF ke sanya wa ido kan rashin daukar matakan yaƙi da safarar kuɗaɗen haram a watan Oktoban 2025.

Haka kuma, Tarayyar Turai ta cire ƙasar daga jerin wuraren da ake kallon suna da babban haɗarin aikata laifukan kuɗi a watan Janairun 2026.

Tinubu ya ce waɗannan matakai na nuna ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa gaskiya a harkokin kuɗi, dawo da amincewar ƙasashen duniya da samar da yanayin da zai taimaka wa halastattun ’yan kasuwa da masu zuba jari.

Shugaban ƙasar ya buƙaci EFCC da sauran hukumomin tabbatar da doka su ci gaba da yaƙi da cin hanci da laifukan kuɗi, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su goyon baya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *