Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci gudanar da bincike cikin gaggawa kuma a bayyane kan hare-haren da aka ce an kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, da ɗan takarar gwamnan Sakkwato na ADC, Manir Muhammad Dan’iya.
A cikin wata sanarwa, Atiku ya bayyana hare-haren a matsayin abin damuwa, yana zargin cewa suna nuna yadda gwamnatin APC ke ƙoƙarin matsa wa ’yan adawa da magoya bayansu lamba.
Ya ce irin waɗannan abubuwa ba su dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
- ADC ta bai wa hukumomin tsaro wa’adin sa’o’i 24 su kama waɗanda suka kai wa ɗan takararta hari a Sakkwato
- Shugaba Tinubu ya ce kamfanin Airtel ya ƙara tashoshin sadarwa 1,050 a Najeriya
Atiku ya kuma zargi wasu masu magoya bayan APC da amfani da ’yan daba wajen tsoratar da abokan hamayyar siyasa, a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu yake gudanar da aikin ibada a ƙasar Saudiyya.
Ya ce yana da sahihan bayanai cewa wasu jami’an wata rundunar tsaro ta cikin gida a Sakkwato na cin zarafin magoya bayan ADC, tare da muzgunawa mutanen da suka sanya kayan jam’iyyar.
Atiku ya kuma nuna damuwa kan ɓacewar wasu fitattun masu amfani da kafafen sada zumunta.
Saboda haka, ya bukaci gwamnatin Tinubu ta tabbatar da gudanar da bincike mai gaskiya kan hare-haren, tare da kare ’yancin ’yan adawa da tabbatar da zaɓe mai ’yanci, gaskiya da gasa.
Ya ce ba za su amince da duk wani yunƙuri na hana ’yan adawa shiga harkokin siyasa a Najeriya ba.