Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da cewa mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Yola, Jihar Adamawa, ba su ɗauke da cutar, bayan gwaje-gwajen da aka gudanar sau biyu a ɗakin binciken lafiya.
Hukumar ta bayyana cewa ta yi aiki tare da gwamnatin Jihar Adamawa wajen gudanar da bincike kan waɗannan mutane, waɗanda aka killace tare da yi musu gwajin cutar.
NCDC ta kuma jaddada cewa mutumin da aka tabbatar ya kamu da Ebola a baya a Babban Birnin Tarayya Abuja shi kaɗai ne aka tabbatar ya kamu da cutar a Najeriya zuwa yanzu.
- Ba gudu ba ja da baya, za mu ƙaddamar da kamfen a Sakkwato – ADC
- NDLEA ta kama masu safarar hodar iblis zuwa Faransa, ta ƙwace harsasai 266 na AK-47
Hukumar ta bukaci ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, tare da dogaro da sanarwar hukumomin gwamnati da na lafiya domin samun sahihan bayanai kan cutar.
Sai dai ta shawarci duk wanda ya fara nuna alamun cutar, kamar zazzabi, matsananciyar kasala, ciwon kai da tsoka, amai, gudawa ko zubar jini ba tare da wani dalili ba, musamman idan ya yi hulɗa da wanda ake zargi, da ya garzaya asibiti.
NCDC ta kuma bukaci masu waɗannan alamomi su sanar da ma’aikatan lafiya tarihin tafiye-tafiyensu da mutanen da suka yi hulɗa da su domin taimakawa wajen tantance yiwuwar kamuwa da cutar.