Wata tawaga mai mambobi bakwai daga Majalisar Dokokin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ziyarci dakarun Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Gambiya, domin duba yanayin rayuwarsu da ƙalubalen da suke fuskanta.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Hon. Edwin Melvin Snowe Jr., ta kai ziyarar ne a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, a sansanin sojojin Najeriya da ke barikin Yundum, inda ta samu tarba daga kwamandan rundunar ECOMIG, Kanal Aliou Tine, da kwamandan dakarun Najeriya, Laftanar Kanal YM Abdullahi.
A yayin ziyarar, ’yan majalisar sun zagaya sansanin, sun duba wuraren kwana da sauran gine-gine, tare da tattaunawa da sojojin domin jin halin da suke ciki.
- SERAP ta bai wa Tinubu wa’adin kwana bakwai a bincike kura-kuran rajistar masu zaɓe
- An tabbatar da babu Ebola a mutane biyu da ake zargi a Adamawa
Daga nan kwamandan dakarun Najeriya ya yi musu bayani kan ayyukansu, shirye-shiryen horarwa, gudanar da mulki da ƙalubalen da suke fuskanta.
Tawagar ta kuma tattauna da jami’an sojin kan yadda za a inganta jin daɗinsu da ayyukansu.
Ziyarar ta kuma ba su damar tantance shirye-shiryen rundunar tsaron Gambiya da ma’aikatun gwamnati wajen karɓar cikakken alhakin tsaron ƙasar, a wani ɓangare na shirin janye dakarun ECOMIG daga Gambiya nan gaba.
A yayin ziyarar, an ba tawagar rigunan tunawa da gangamin wayar da kai kan cutar kansar mama na watan Oktoba na shekarar 2026, wanda dakarun Najeriya ke gudanarwa, ciki har da gwaje-gwajen lafiya a asibitin rundunar.
A jawabinsa, Edwin Melvin Snowe Jr. ya ce za su isar da ƙorafe-ƙorafe da matsalolin gine-ginen da suka gani ga hukumomin da abin ya shafa domin a ɗauki matakan inganta rayuwa da jin daɗin sojojin da ke aikin.