Gwamnatin Jihar Ekiti ta ɗauki ma’aikatan lafiya guda 1,522 domin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a cibiyoyin kula da lafiya matakin farko a faɗin jihar.
Shugabar Hukumar Bunƙasa Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Jihar Ekiti, Dakta Funke Ogunbunmi, ta bayyana ɗaukar ma’aikatan a matsayin wani babban mataki na magance ƙarancin ma’aikata da kuma inganta muhimman ayyukan kiwon lafiya a matakin ƙananan hukumomi da al’ummomi.
- Sojojin sama 816 sun kammala atisayen gwajin juriya a Kaduna
- SERAP ta bai wa Tinubu wa’adin kwana bakwai a bincike kura-kuran rajistar masu zaɓe
- An tabbatar da babu Ebola a mutane biyu da ake zargi a Adamawa
Ogunbunmi, a cikin wata sanarwa da ta fitar a Ado-Ekiti ranar Lahadi 1/11/2026, ta yaba wa Gwamna Biodun Oyebanji bisa amincewa da ɗaukar ma’aikatan, inda ta ce matakin ya nuna jajircewarsa wajen bai wa lafiyar al’ummar jihar muhimmanci ta hanyar zuba jari a ɓangaren kiwon lafiya.
Ta tabbatar da aniyar hukumar ganin cewa sabbin ma’aikatan sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan kiwon lafiya da kuma samar da sakamako mai kyau a fannin kula da lafiyar al’umma a jihar.
Ta bayyana cewa ana ci gaba da bayar da takardun ɗaukar aiki ga waɗanda suka yi nasara a cikin rukunin masu taimakawa ayyukan gwaje-gwajen lafiya (Laboratory Assistants), mataimakan ma’aikatan lafiya (Health Assistants) da masu kula da marasa lafiya (Health Attendants).