Jam’iyyar African Action Congress (AAC) ta nemi gwamnatin Jihar Ekiti da rundunar ’yan sandan jihar su yi bayani kan yadda aka gano wayar wani mamba a tawagar ɗan takararta na shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, kusa da gidan gwamnatin jihar bayan harin da aka kai musu a Ado-Ekiti.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Rex Elanu, ya fitar, AAC ta ce an rasa wayar ne bayan harin da aka kai wa Sowore da tawagarsa a ranar Juma’a, amma daga baya aka gano inda take ta hanyar bin diddiginta.

Jam’iyyar ta ce an gano wayar a kusa da gidan gwamnan jihar, tare da neman hukumomi su bayyana yadda ta isa wurin da kuma mutanen da suka shiga lamarin.

AAC ta kuma buƙaci hukumomin tsaro su fitar da hotunan kyamarorin CCTV da ke wurin da aka kai harin, domin taimakawa bincike da tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

Ta kuma nemi gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, tare da kare dukkan hujjoji da tabbatar da cewa waɗanda aka samu da hannu a harin sun fuskanci hukunci.

A halin yanzu, ana ci gaba da ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin Jihar Ekiti da rundunar ’yan sandan jihar kan zarge-zargen da jam’iyyar ta gabatar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *