Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin tauye dimokuraɗiyya da ’yancin ’yan Najeriya na shiga harkokin siyasa, tana mai cewa yunƙurin murƙushe ’yan adawa ba zai yi nasara ba.
A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC-PCC ta ce abubuwan da ke faruwa a sassan ƙasar sun wuce rikicin siyasa na yau da kullum, domin a cewarta, akwai alamun tsoratarwa, cin zarafi da danne muryoyin ’yan adawa.
Majalisar ta lissafa hare-haren da ta ce an kai wa shugabanni da mambobinta a Kaduna, zargin dukan ɗan takararta na gwamnan Sakkwato, Alhaji Munir Dan Iya, da jami’an ’yan sintiri na jihar a kan titin Airport Road, da kuma rushe ofishin yaƙin neman zaɓenta a Kebbi.
- Kwankwaso ya zargi wasu ’yan hamayya da ƙoƙarin cire sunan Gwarzo daga jerin ’yan takarar Kano
- Sarki Charles zai yi magana kan cinikin bayi a taron ƙasashen Commonwealth
Ta kuma ambaci zargin hana ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, amfani da wurin kamfen a Enugu, da hare-haren da aka ce an kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC, Omoyele Sowore.
ADC-PCC ta kuma nuna damuwa kan ci gaba da tsare mataimakin shugabanta, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tana zargin ana tsare da shi ba bisa ƙa’ida ba tare da hana shi damar samun beli.
Ta kuma yi zargin cewa ana amfani da kuɗi da wasu abubuwan ƙarfafawa domin raunana ’yan adawa, tana mai cewa ’yan Najeriya ba za su sayar da ’yancinsu na siyasa ba.
Majalisar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su tsaya tsayin daka wajen kare dimokuraɗiyya, ’yancin haɗa kai da kuma damar zaɓar jam’iyyar da suke so.
Ta ce ADC za ta ci gaba da fafutukar samar da wani zaɓi na siyasa, tana mai cewa ba za a iya murƙushe burin al’umma ba, kuma dimokuraɗiyya za ta yi nasara.