Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan dakarun sojin Operation Enduring Peace (OPEP) a wani shingen bincike da ke ƙaramar hukumar Riyom ta Jihar Filato, inda suka kashe soja ɗaya tare da kwashe makamai guda biyu.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Asabar a shingen binciken sojoji na Sopp, da ke Ungwan Boka, a ƙaramar hukumar Riyom.
An ruwaito cewa sojojin na tsaye suna aikin tsaro a shingen ne lokacin da maharan suka buɗe musu wuta daga wurare daban-daban, lamarin da ya haddasa musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.
-
Kwankwaso ya zargi wasu ’yan hamayya da ƙoƙarin cire sunan Gwarzo daga jerin ’yan takarar Kano
-
AAC ta nemi a bayyana yadda aka gano wayar tawagar Sowore kusa da gidan gwamnan Ekiti
-
Sojojin sama 816 sun kammala atisayen gwajin juriya a Kaduna
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ƴan bindigar sun tsere zuwa cikin dazukan da ke kewaye da yankin bayan musayar wutar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya bayyana harin a matsayin wanda aka kai da gangan ba tare da wani dalili ba.
Ya ƙara da cewa sojojin sun samu nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Kyaftin Oteh ya ce har yanzu ana kula da yanayin tsaro a yankin, yayin da sojoji ke ci gaba da tsaurara sa ido domin hana sake samun irin wannan matsalar tsaro da kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa suna cikin aminci.
