Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ta soki yunƙurin da ta ce na sake fassara alƙawarin Shugaba Bola Tinubu na samar da wutar lantarki a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, tana mai cewa babu wani bayani da zai iya sauya alƙawari da ya yi wa ’yan Najeriya .
A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC-PCC ta mayar da martani ga kalaman Dele Alake, mai magana da yawun majalisar yaƙin neman zaɓen APC, inda ce Tinubu ya bayyana karara cewa idan bai samar da wutar lantarki ba a wa’adinsa na farko, kada ’yan Najeriya su sake zaɓensa a wa’adi na biyu.
Majalisar ta ce maimakon kawo ƙarshen tsarin ƙiyasin kuɗin wuta, gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗin lantarki, lamarin da ta ce ya jefa gidaje cikin wahalar biyan kuɗin wutar.
- ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da tauye ’yancin siyasa a Nigeria
- Filato: ’Yan bindiga sun kashe soja ɗaya tare da kwashe makamai
ADC-PCC ta kuma soki tsarin rarraba masu amfani da wuta zuwa rukunan Band A, B, C da sauransu, tana mai cewa ana karɓar ƙarin kuɗi ba tare da samar da ingantacciyar wuta ba.
Ta ce ’yan Najeriya na fuskantar katsewar wuta, rugujewar babban layin rarraba wuta na ƙasa da ƙarancin wutar lantarki, duk da shirye-shiryen da gwamnati ta sanar, ciki har da shirin samar da mitoci.
Majalisar ta ce dogaro da dokar samar da wutar lantarki da shirye-shiryen lamuni wajen kare ayyukan gwamnati ba ya amsa tambayar ko ’yan Najeriya na samun wutar lantarki mai araha kuma abin dogaro.
Ta yi kira ga jam’iyyar APC da ta yi bayani kan rashin cika alƙawarin, tana mai cewa zaɓen 16 ga Janairu, 2027, zai ba ’yan Najeriya damar tantance ayyukan gwamnati da alƙawuran da ta ɗauka.