Sojojin Najeriya sun ce sun kashe wasu ’yan ƙungiyar Daesh da dama, ciki har da mamba a majalisar Shura da wani babban kwamanda, yayin wani artabu a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Sanarwar da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Lahadi, ta ce lamarin ya faru ne a ranar 31 ga Oktoba, 2026, bayan ’yan ta’addan sun kai hari kan sansanonin sojoji da ke yankin.

Sojojin sun bayyana sunayen manyan mutanen da aka kashe a matsayin Abu Hajara, mamba a majalisar Shura ta ƙungiyar, da Abul Walid, kwamanda kuma na kusa da Ba Shuwa, wanda sanarwar ta bayyana a matsayin babban jagoran Daesh.

A cewar sanarwar, sojojin sun yi amfani da dakarun ƙasa da tallafin jiragen yaƙi wajen dakile harin, inda suka ƙwato makamai, alburusai da na’urorin sadarwa.

Wannan na zuwa ne ƙasa da kwanaki uku bayan wani samamen soji a Buni Yadi, inda sojojin suka ce sun kashe ’yan ta’adda 55, ciki har da wasu manyan kwamandoji.

Operation HADIN KAI ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda domin kare fararen hula da lalata sansanoninsu.

Sai dai babu tabbaci mai zaman kansa da ya tabbatar da ikirarin sojojin kan adadin waɗanda aka kashe da kuma matsayinsu a ƙungiyar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *