Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta samu gagarumar nasara a kan Liverpool, bayan ta doke ta da ci 1-0 a filin wasa na Anfield, a fafatawar gasar Firimiya ta Ingila.
Kai Havertz ne ya ci wa Arsenal ƙwallonta a minti na 16, inda ta riƙe wannan ƙwallo har zuwa ƙarshen wasan, duk da ƙoƙarin da Liverpool ta yi na farkewa.
A yayin wasan, Liverpool ta fi Arsenal mallakar ƙwallo da kaso 56.2 bisa 43.8, sannan ta samu bugun ƙwallo sau takwas, yayin da Arsenal ta samu biyar.
- An tabbatar da Samson Adamu a matsayin Babban Sakataren Hukumar CAF
- Gasar Cin Kofin Duniya ta U15: Najeriya ta doke New Caledonia da Ci 7-0
Sai dai Arsenal ta fi Liverpool bugun ƙwallon da ya nufi raga, inda ta samu biyu, ita kuma Liverpool ba ta samu ko guda ba.
A ra’ayin tsohon ɗan wasan Arsenal, Ian Wright, dole ne ƙungiyar ta taka a hankali tare da kare ragarta, saboda Liverpool za ta matsa mata lamba a rabin lokaci na biyu.
Ya kuma bayyana cewa Arsenal za ta iya cin moriyar guraben da Liverpool za ta bari wajen kai hare-haren bazata.
Nasarar ta kasance ta musamman ga Arsenal, domin ita ce ta farko da ta samu a gidan Liverpool cikin shekaru 14.
Haka kuma, sakamakon ya mayar da Gunners saman teburin gasar Firimiya ta Ingila.