Mutane tara sun mutu bayan wani ƙaramin jirgin sama kirar Learjet 60 ya yi hatsari a wani unguwa da ke jihar Florida ta Amurka a ranar Lahadi, kamar yadda Sakataren Sufuri na ƙasar, Sean Duffy, ya bayyana.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:50 na rana agogon yankin, kusa da Cresthaven, mai tazarar kilomita 14 daga gidan shakatawa na Mar-a-Lago mallakin Shugaba Donald Trump da ke Palm Beach County.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta ce jirgin ya tashi ne daga Austin da ke jihar Texas, yana kan hanyarsa ta zuwa Bahamas.
- ADC ta ce babu hujjar da za ta ɓoye gazawar Tinubu wajen samar da wutar lantarki
- Shugaban Majalisar Wakilai zai bayyana ayyukan majalisa ta 10 a shirin talabijin
Hotunan wurin sun nuna wani babban rami a kan titin unguwa, tare da tarkacen jirgin da wasu sassan siminti sun watse a wurin.
Sakataren Sufuri Sean Duffy ya bayyana lamarin a matsayin mummunan bala’i, yana mai cewa FAA za ta tura tawaga domin taimakawa Hukumar Binciken Hatsarin Sufurin Jiragen Sama (NTSB) wajen gudanar da bincike.
Hukumar kashe gobara ta Palm Beach County ta ayyana lamarin a matsayin babban hatsari da ya shafi mutane da dama.
Har yanzu ba a bayyana sunayen mutanen da ke cikin jirgin ba, kuma ba a tabbatar ko akwai waɗanda suka jikkata ko suka mutu a ƙasa ba.
Hukumomin yankin sun shawarci masu ababen hawa da su guji hanyar da hatsarin ya faru domin kauce wa cunkoso.