Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Majidadin Daular Usmaniyya, ya taya Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekara 20 a kan karagar mulkin masarautar Sakkwato.
A cikin saƙon taya murnar, Pantami ya bayyana shekaru 20 na Sarkin Musulmi a kan karagar mulki a matsayin lokacin da ya nuna hikima, tawali’u, jajircewa wajen bunƙasa ilimi da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
- Mutane tara sun mutu a wani hatsarin Jirgin sama a Florid
- Tinubu ya gana da tawagar Najeriya a Makka, sun yi alƙawarin tallafa wa gwamnatinsa
Ya kuma yaba da rawar da Sarkin Musulmi ke takawa wajen inganta zaman lafiya tsakanin addinai, kare muradun talakawa da kuma ƙarfafa haƙuri da zaman tare tsakanin al’umma.
Pantami ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Sarkin Musulmi lafiya, hikima da ƙarfi domin ci gaba da hidimar masarautar Sakkwato da al’umma da kuma Najeriya baki ɗaya.