Ƙungiyoyin direbobin motocin haya da na kasuwanci a Ghana sun sanar da tsayar da zirga-zirgar motocinsu a faɗin ƙasar ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026, domin nuna rashin amincewarsu da tsarin tara kuɗin TRAFFITECH-GH da kuma cinikayyar da ake yi a tashoshin mota.

Sanarwar da aka fitar ranar 1 ga Nuwamba, mai ɗauke da sa hannun shugabannin ƙungiyoyi biyar, ciki har da Ghana Private Road Transport Union (GPRTU), ta ce babu motar kasuwanci da za ta yi aiki a ranar da aka ayyana yajin aikin.

Ƙungiyoyin sun zargi gwamnatin Ghana da rundunar ’yan sanda da gaza aiwatar da ƙa’ida ta 142 ta dokokin zirga-zirgar ababen hawa na shekarar 2012, wadda ta haramta cinikayya a tashoshin mota da kuma hanyoyin da aka tanada domin masu tafiya a ƙasa.

Sun ce ’yan kasuwa sun mamaye wuraren da aka ware domin motocin haya su tsaya, lamarin da ke hana direbobi gudanar da aikinsu yadda ya kamata, amma duk da haka ana ci gaba da amfani da na’urorin TRAFFITECH-GH wajen gano laifuffuka da ci musu tara.

Ƙungiyoyin sun nemi direbobi su ajiye motocinsu a ranar Laraba har sai an samu sabon umarni.

Sun kuma ba da haƙuri ga fasinjoji kan matsalar da yajin aikin zai iya haifarwa, tare da shawartar su da su nemi wasu hanyoyin zirga-zirga.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *