Mutane takwas sun mutu, yayin da aka ceto wasu 21 bayan wata motar fasinja mallakar ’yan ƙasar Ivory Coast ta yi karo da motar Burkina Faso da aka ajiye a gefen hanya a Ghana.
- Pantami ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekara 20 a kan karagar mulki
- Mutane 9 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Florida
Hatsarin ya faru ne a yankin Azuletti, kusa da Samenye, a kan babbar hanyar Elubo zuwa Takoradi.
Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasar Ghana (GNFS) ta ce binciken farko ya nuna cewa gudun wuce gona da iri na iya kasancewa cikin abubuwan da suka haddasa hatsarin.