Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wani mutum mai shekara 42 bisa zargin satar motar Toyota Corolla LE da ke ɗauke da kayayyaki da kuɗaɗe na miliyoyin Naira a Maiduguri.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Oktoba, 2026, lokacin da wani mai harhaɗa magunguna, Abdulwahab Muhammed, ya ajiye motarsa a kan titin Muna domin gudanar da sallah. Bayan dawowarsa, sai ya tarar an sace motar.
Sanarwar ta ce motar na ɗauke da kwamfutar hannu ta Redmi, kuɗin Naira 230,000 da dala 200, kayayyakin magunguna da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 3.3, da kuma katin ATM.
- NIMC ta kama waɗanda ake zargi da gudanar da rajistar NIN ba bisa ƙa’ida ba
- ’Yan bindiga sun sace ɗaliban makarantar Islamiyya 14 a Jihar Neja
Bayan samun rahoton, kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya umarci jami’an sashen yaƙi da laifuka masu tsanani na rundunar da su gudanar da cikakken bincike.
Binciken ya kai ga kama wanda ake zargi, wanda aka samu a hannunsa da motar da kayayyakin da aka sace.
A yayin binciken farko, wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi amfani da wani makulli ne wajen buɗe motar kafin ya tafi da ita.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike, yayin da ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ta buƙaci mazauna jihar da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka gani na zargi, tare da bayar da bayanan da za su taimaka wa jami’an tsaro.