Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wata illa da suka lura magani ya haifar musu, domin taimakawa wajen inganta tsaron magunguna da kare lafiyar sauran masu amfani da su.
Hukumar ta bayyana hakan ne yayin makon wayar da kan jama’a kan tsaron magunguna na duniya na shekarar 2026, wanda za a gudanar daga 2 zuwa 8 ga watan Nuwamba, ƙarƙashin taken MedSafetyWeek.
WHO ta ce illar magani na iya haɗawa da kaikayin fata ko kuraje, matsalar ciki, rashin samun barci ko sauyin yanayin tunani.
- Sojoji sun tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane a Kogi, sun kwato harsasai 1,000
- Gwamna Kefas ya bai wa mafarauta babura 40 domin ƙarfafa tsaron kan iyakar Taraba
Ta kuma bayyana cewa irin waɗannan matsaloli na iya bayyana jim kaɗan bayan fara shan magani, bayan dogon lokaci ko kuma sakamakon haɗa magunguna daban-daban.
Hukumar ta jaddada cewa ko da an gwada magani sosai kafin a fara sayar da shi, akwai yiwuwar ya haifar da wasu illoli da ba a yi tsammani ba. Saboda haka, likitoci da masana kimiyya na ci gaba da sa ido kan lafiyar magunguna bayan sun shiga kasuwa.
Ta shawarci duk wanda ya lura da wata matsala bayan shan magani da ya tuntubi ƙwararren ma’aikacin lafiya, sannan ya kai rahoto ta tsarin bayar da rahoton illolin magunguna na ƙasarsa, ko da kuwa bai tabbatar cewa maganin ne ya jawo matsalar ba.
WHO ta ce duk rahoton da aka gabatar na taimakawa masana wajen gano haɗurran da ka iya tattare da magunguna, tare da ɗaukar matakan kare sauran masu amfani da su.