Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya samar da babura 40 domin tallafa wa mafarauta wajen gudanar da sintiri da inganta tsaro a al’ummomin da ke kan iyakar ƙaramar hukumar Karim Lamido, bayan harin da aka kai garin Binnari.

Kwamishiniyar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma ta jihar, Zainab Usman Jalingo, ta bayyana cewa an samar da baburan ne tare da tallafin man fetur da abinci domin sauƙaƙa wa mafarautan gudanar da ayyukansu a yankunan da ke da wahalar zirga-zirga.

Ta ce matakin na zuwa ne bayan wani taron tsaro da gwamnan ya kira bayan harin Binnari, inda wakilan al’umma suka bayyana cewa mafarautan yankin za su iya taimakawa wajen dakile hare-hare da hana masu laifi zirga-zirga idan aka samar musu da hanyoyin sufuri.

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayar da umarnin samar da baburan domin tallafa wa mafarauta a Andamin, Jukun, Binnari, Belango, Jebjeb, Garau da sauran al’ummomin da ke kan iyaka.

Kwamishiniyar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar na shirin buɗe hanyoyi domin sauƙaƙa isa ga al’ummomin da ke keɓe, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da jihohin da ke makwabtaka da Taraba da rundunonin soji.

Ta ce matakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *