Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kammala ziyarar Umrah da ya kai ƙasar Saudiyya, inda ya ce shi da mambobin tawagarsa sun samu damar shiga cikin Ka’aba mai alfarma domin yin addu’a.
A cikin saƙon da ya wallafa bayan kammala ziyarar, Tinubu ya bayyana cewa sun kuma gudanar da ibadar Umrah, tare da samun damar shiga Ka’aba, lamarin da ya bayyana a matsayin wata dama ta musamman.
- Gwamna Uba Sani ya shiga cikin Ka’aba tare da Tinubu a Makka, ya yi addu’ar zaman lafiya ga Najeriya
- Tinubu ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekara 20 a kan karagar mulki
Shugaban Ƙasar ya gode wa Mai Kula da Masallatai Masu Alfarma Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado kuma Firaministan Saudiyya, Mohammed bin Salman, bisa damar da suka ba su da kuma kyakkyawar tarbar da suka yi wa tawagar.
Ya ce wannan karamci na nuna ƙarfafa dangantakar addini da abota da ke tsakanin Najeriya da Saudiyya, yana mai bayyana godiyarsa ga kulawa da tarbar da suka samu yayin ziyarar.
Tinubu ya ce a lokacin da suke cikin wannan wuri mai tsarki, ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Najeriya da daukacin al’ummar ƙasar.