Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa damar shiga cikin ɗakin Ka’aba mai alfarma da ke Makka tare da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da sauran mambobin tawagar Najeriya.

Gwamnan ya kuma gode wa Mai Kula da Masallatai Masu Alfarma Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa wannan dama da suka ba wa Shugaban Ƙasa da tawagarsa.

A cikin Ka’aba, Uba Sani ya ce ya yi addu’a ga Jihar Kaduna, al’ummarta da kuma Najeriya baki ɗaya, yana roƙon Allah Ya saukar da rahama, shiriya da albarka domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma roƙi Allah Ya karɓi addu’o’insu, Ya ƙara musu tawali’u tare da ƙarfafa musu ƙudurin yi wa al’ummar da suke jagoranta hidima cikin gaskiya da riƙon amana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a saƙon da ya wallafa, inda ya nuna godiyarsa bisa wannan dama da ya samu na shiga cikin Ka’aba tare da Shugaban Ƙasa da sauran tawagar Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *