Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekara 20 a kan karagar mulkin Sarkin Musulmi na 20, inda ya yaba da gudunmawarsa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kan Najeriya.
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, Tinubu ya bayyana cewa Sarkin Musulmi ya hau karagar mulki ne shekaru 20 da suka gabata cikin tawali’u, jarumtaka da sanin nauyin da ke kansa.
Shugaban Ƙasar ya ce a tsawon 20 da suka gabata, Sarkin Musulmi ya kiyaye martabar Daular Usmaniyya tare da bunƙasa ta, inda ya mayar da ita wata kafa ta inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
- ’Yan sanda sun fara shirin horas da jami’ai 10,000 kan tsaron zaɓen 2027
- Gwamna Uba Sani ya shiga cikin Ka’aba tare da Tinubu a Makka, ya yi addu’ar zaman lafiya ga Najeriya
Tinubu ya kuma yaba da hikimar Sarkin Musulmi, jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya a lokutan da ake fuskantar tashin hankali, da kuma ƙoƙarinsa na inganta fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Ya ce a matsayinsa na shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, da kuma mataimakin shugaban Hukumar NIREC, ya taka rawa wajen ƙarfafa zaman tare tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Ya ƙara da cewa ƙoƙarin Sarkin Musulmi wajen samar da zaman lafiya a Arewa da yankin Sahel, inganta ilimi musamman na ’ya’ya mata, tallafa wa manoma da lafiyar al’umma, da kuma taimaka wa marasa ƙarfi, na nuna yadda mulkinsa ya mayar da hankali kan jin daɗin jama’a.
Tinubu ya kuma bayyana godiyarsa bisa abota, shawarwari da addu’o’in da Sarkin Musulmi ke yi wa Najeriya.