Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da su fafata a gasar kawo nassosin Alƙur’ani, bayan ziyarar Umrah da shugaban ya kai ƙasar Saudiyya.
Melaye ya bayyana ƙalubalen ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, inda ya ce a shirye yake su yi wannan gasar da Tinubu bayan dawowarsa daga Saudiyya.
- Mutane 8 sun mutu a hatsarin mota tsakanin Ghana da Burkina Faso
- Gwamna Uba Sani ya shiga cikin Ka’aba tare da Tinubu a Makka, ya yi addu’ar zaman lafiya ga Najeriya
A cikin saƙon, Melaye ya ce: “Yanzu da Alhaji Bola Tinubu yake gudanar da Umrah, ina ƙalubalantarsa da zarar ya dawo, mu fafata a gasar kawo ayoyin Alƙur’ani. Babu wanda zai yi wa Allah ba’a.”
Ƙalubalen na zuwa ne bayan Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa bayanai kan ibadun Tinubu a Saudiyya, ciki har da shiga cikin Ka’aba mai alfarma da ke Makka, kamar Jaridar Punch ta rawaito.