Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce ta samu nasarorin ayyukan tsaro a jihohi daban-daban cikin sa’o’i 24, ciki har da ceto wata matashiya daga hannun fusatattun jama’a a Jihar Adamawa, bayan zargin jefa wani yaro mai shekara uku cikin rijiya da ya yi sanadin mutuwarsa.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ƙauyen Shuwa da ke ƙaramar hukumar Madagali, inda aka ceto gawar yaron bayan ƙoƙarin aikin ceto na sa’o’i.

Rundunar ta ce jama’a sun yi yunƙurin kashe matashiyar tare da ƙona ta, amma jami’an ’yan sanda suka kuɓutar da ita. An miƙa binciken lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na Yola.

A Jihar Osun kuwa, ’yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da kashe wani dattijo mai shekara 67 da adda, bayan saɓani kan kuɗi Naira 10,000.

A Borno kuma, an gano gawarwakin wasu ’yan’uwa biyu da raunukan kibiyoyi a jikinsu, yayin da a Bauchi ake neman wani mutum da ake zargi da caka wa wani matashi wuƙa har ya mutu.

Haka kuma, ’yan sanda na neman waɗanda ake zargi da kashe wani mutum a rikicin ƙungiyar asiri a Cross River.

A Jihar Neja, mutane biyu sun mutu bayan kwale-kwale ya kife a Kogin Dogo yayin da suke ƙoƙarin zuwa gonakinsu.

Haka kuma, an gano gawar wani matashi da ba a san ko wanene shi ba a Suleja, yana da raunin sara a ƙirjinsa.

A Osun kuma, ’yan sanda na binciken fashin da wasu mutane sanye da kayan sojoji suka aikata a babbar hanyar Ife zuwa Osu.

A Ogun, rundunar na binciken mutuwar wani ɗan ƙasar China mai shekara 44 da ya mutu bayan ya koka da rashin lafiya.

A Akwa Ibom kuma, ’yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da satar wayoyin lantarki da sandunan ƙarfe daga wani wurin gine-gine a Uyo, bayan jami’ai sun tare babur mai kafa uku da suke ciki.

Rundunar ta ce ta kama mutum huɗu, sannan an samu laifukan kisan kai guda bakwai, fashi da makami guda ɗaya da kuma laifin ƙungiyar asiri guda ɗaya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *